Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-28 19:31:35    
Kasar Sin za ta yi la'akari da halartar taron koli kan kasuwannin kudi da tattalin arzikin duniya na G20

cri
Ran 28 ga wata, a gun taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing, Jiang Yu, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ta bayyana cewa, kasar Sin ta riga ta samu gayyatar da kasar Amurka ta yi mata game da halartar taron koli kan kasuwannin kudi da tattalin arzikin duniya da shugabannin kasashe mambobin kungiyar G20 za su yi, kuma za ta yi la'akari da gayyatar a tsanake.

An labarta cewa, Amurka za ta kira taron koli na shugabannin mambobin kungiyar G20 a birnin Washington a ran 15 ga wata domin yin tattaunawa kan matsalar kudi da ta ratsa duk duniya.

Madam Jiang ta kara da cewa, matsalar kudi da ake fuskanta a yanzu ta nuna cewa, yana iya kasancewa rashin tafiyar da abubuwa yadda ya kamata a cikin tsarin sha'anin kudi na duniya da ake bi a yanzu, kana kuma, tsarin sha'anin kudi na duniya yana nuna gazawa a wasu fannoni. Kamata ya yi kasashen duniya su yi gyare-gyare kan tsarin sha'anin kudi na duniya daga dukkan fannoni bayan da dukkan bangarorin da abin ya shafa suka yi shawarwari. Ban da wannan kuma, ya kamata su sa kaimi kan kafa tsarin sha'anin kudi na duniya cikin adalci, wanda zai kula da moriyar dukkan bangarori, ta haka zai ba da babban tabbaci wajen ci gaba da raya tattalin arzikin duniya ba tare da tangarda ba.

Dadin dadawa kuma, madam Jiang ta yi kira a inganta sa ido kan sha'anin kudi a duniya, da sa kaimi wajen yin gyare-gyare kan hukumomin kudi na duniya da kuma kara bai wa kasashe masu tasowa ikon bayyana ra'ayoyinsu a cikin kungiyoyin kudi na duniya.(Tasallah)