Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-26 20:29:19    
Bankin duniya da hukumar samun bunkasuwa ta Faransa za su samar da rancen kudi kusan dala biliyan daya ga yankuna masu fama da girgizar kasa na Sin

cri
Wakilan bankin duniya da hukumar samun bunkasuwa ta kasar Faransa sun yi bayani a ran 26 ga wata a lardin Sichuan da ke yammacin kasar Sin, cewar za a samar da rancen kudi da yawansu zai kai dala miliyan 710 da miliyan 200 bi da bi ga lardin Sichuan da sauran yankuna masu fama da girgizar kasa wajen sake farfado da muhimman ayyukan yau da kullum da dai sauransu.

Ede Jorge Ijjasz-Vasquez, shugaban hukumar kula da ayyukan samun dauwamammiyar bunkasuwa na Sin da Mongolia na bankin duniya ya yi bayani a gun taron tattaunawa kan zuba jari da hadin gwiwa tsakanin kungiyar tarayyar Turai da lardin Sichuan, cewar bankin duniya yana cikin shirin samar da rancen kudi dala miliyan 710 ga lardunan Sichuan da Gansu masu fama da girgizar kasa waje shimfida hanyoyi da gadoji da gina asibitoci da makarantu.

Ban da wannan kuma, hukumar samun bunkasuwa ta kasar Faransa tana cikin shirin samar da rancen kudi dala miliyan 200 ga lardin Sichuan domin raya muhimman ayyukan yau da kullum na birane da kuma gina dakunan kwana na kauyuka.(Kande Gao)