Ran 21 ga watan, kakakin ma'aikatar tsaron zaman lafiya ta kasar Sin Mr. Wu Heping ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, an tabbatar da mambobi 8 na kungiyar Musulmi ta gabashin Turkiya a matsayin 'yan ta'adda na jeri na 2 na kasar.
Wu Heping ya bayyana cewa, bisa kudurin M.D.D wajen yaki da ta'adanci, an ce, bayan da aka yi bincike a kansu da tantance su, an tabbatar da Memetiming Memeti da sauran mutane a matsayin 'yan ta'adda na kasar. Yana fatan kasashen da abin ya shafa da hukumomin mulki za su gudanar da bincike ga wadannan 'yan ta'adda,da zarar aka gansu, sai a cafke su a mika su zuwa gwamnatin kasar Sin.
Bisa labarin da muka samu, an ce, tun daga shekarar bara, 'yan ta'adda na kungiyar Musulmi ta gabashin Turkiya sun kulla makarkashiya kuma sun aikata manyan laifuffuka a jere a gida da waje, kuma ya kawo babban lahani ga tsaron gasar wasannin Olympic ta Beijing da zaman karko a zamantakewar al'umma ta kasar Sin.(Bako)
|