Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-13 22:02:10    
Hu Jintao yana fatan wadanda ba 'yan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ba su bayar da ra'ayoyinsu wajen yin gyare-gyare a kauyuka

cri
A kwanan baya, Mr. Hu Jintao, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya yi fatan wadanda ba 'yan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ba za su iya bayar da ra'ayoyi da shawara kan yadda za a karfafa da kuma kyautata ayyukan da ake yi a kauyuka domin neman sabbin matakai da hanyoyin yin gyare-gyare da neman cigaba a kauyuka.

A gun taron tattaunawa da kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya kira kwanan baya, Hu Jintao ya saurari jawaban da wadanda ba 'yan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ba suka yi kan yadda za a kara raya kauyukan kasar Sin. Hu Jintao ya ce, daidaita batutuwan aikin gona da kauyuka da manoma nauyi ne mafi muhimmanci daga cikin muhimman nauyin da ke bisa wuyan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma muhimman batutuwa ne da ke bisa wuyan dukkan jam'iyyun siyasa da ke daidaita da kuma tattaunawa kan harkokin siyasa tare da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin. Yana fatan jam'iyyun siyasa da ba na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ba za su ci gaba da yin amfani da sharadinsu mai karamci, wato suna da kwararru da masana masu dimbin yawa a fannoni iri iri domin kara yin bincike kan batutuwa ta yadda za a kirkiro sabon tsarin kauyuka da raya aikin gona na zamani da ciyar da kauyuka gaba daga dukkan fannoni. Haka kuma, za su iya gano matsaloli masu tsanani da ke kasancewa a kauyuka lokacin da ake yin gyare-gyare da neman cigaba a kauyuka da kuma gabatar da shawara da ra'ayoyinsu kan yadda za a daidaita irin wadannan matsaloli. Hu Jintao ya kara da cewa, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin za ta yi nazari kan shawara da ra'ayoyi masu daraja kuma masu inganci, har ma za ta yi amfani da su. (Sanusi Chen)