Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-07 15:13:47    
Gasar wasannin Olympic ta Beijing ta canja ra'ayin mutanen kasashen waje a kan kasar Sin

cri
Bisa sakamakon wani bincike da aka yi mai suna "ganin mutanen kasashen duniya a kan kasar Sin", an ce, gasar wasannin Olympic ta Beijing ta canja ra'ayin mutanen kasashen waje a kan kasar Sin.

An yi wannan bincike ta hanyar yin hira a kan hanya da bin bahasi a kan Internet, kuma galiban mutanen da aka yi hirar da su mutanen kasashen ketare ne da suka zo kasar Sin a lokacin gasar wasannin Olympic ta Beijing. Bisa sakamakon da muka samu a cikin wannan bincike, an ce, kafin su zo kasar Sin, akasarin mutanen kasashen waje sun dauki Sin kamar wata kasa mai ban mamaki, mai dogon tarihi a gabashin duniya, kuma sun sami dukkan wadannan ra'ayoyi daga kafofin yada labaru na kasashensu, da sauran litattafai, da labarun da aka gaya musu. A lokacin gasar wasannin Olympic ta Beijing, yawancin mutanen kasashen waje sun ganewa idanunsu zaman rayuwar Sinnawa, da dakuna da filayen wasannin Olympic na zamani, da shirya gasar wasannin Olympic cikin nasara, kuma sun kara ilmi wajen nasarorin da Sin ta samu, kuma sun san yadda kasar Sin take kai tsaye. Kashi 60 cikin kashi 100 na mutanen da suka amince a yi hirar da su, suna ganin cewa, a cikin shekaru 20 masu zuwa, Sin za ta zama kasa mafi saurin bunkasuwar tattalin arziki a duniya. 

Game da abin da zai iya wakiltar China, mutanen kasashen waje sun zabi "babbar ganuwar Sin watau Great Wall" da "wasan Chinese Kongfu" da "Abincin China". Amma yawancin mutanen kasashen waje ba su san "abubuwa hudu da Sin ta kago ba watau wasannin wuta na Gunpowder da hanyoyin yin takarda watau Papermaking da hanyoyin gurzawa watau Commercial Printing da Compass. Yawan mutanen da suka zabi likitancin gargajiya na Sin da zai iya wakiltar China ya kai kashi 2 cikin kashin 100.

Abin da ya kamata mu mai da hankali shi ne, ko da tattalin arzikin China na bunkasuwa cikin hanzari, amma sama da kashi 60 cikin kashin 100 na mutanen kasashen waje da muka yi hira da su, suna ganin cewa, bunkasuwar tattalin arzikin China ta haifar da matsaloli masu yawa, ala misali, matsalar yanayi. Wannan ya nuna cewa, ko da yake Sin ta yi iyakacin kokari wajen kiyaye muhalli, amma har yanzu tsugune ba ya kare ba.(Bako)