Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-10-06 16:35:03    
Ana farfado da kasuwar yawon shakatawa a lardin Sichuan

cri

Ana farfado da kasuwar 'yawon shakatawa a lardin Sichuan bayan bala'in girgizar kasa mai tsanani. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, a kwanaki 6 na farkon lokacin hutu na bikin murnar kafuwar kasar Sin, wato daga ran 29 ga watan Satumba zuwa ran 4 ga watan Oktoba, wuraren yawon shakatawa 20 na lardin Sichuan sun karbi masu yawon shakatawa da yawansu ya kai dubu 990, inda aka samu kudin Sin RMB Yuan fiye da miliyan 68.

A cikin wadannan kwanaki 6, wurin yawon shakatawa na Jiuzhaigou-Huanglong ya karbi masu yawon shakatawa fiye da dubu 60. Yawan 'yan yawon shakatawa da suka fito daga biranen Beijing da Shanghai da Guangzhou da sauran birane masu nisa ya karu, wurin Jiuzhaigou ya sake fara jawo 'yan yawon shakatawa.

Kazalika, wurin yawon shakatawa na dusen Qingcheng da madatsar ruwa ta Dujiangyan dake yanki mafi fama da bala'in girgizar kasa ya sake bude kofa ga 'yan yawon shakatawa, a wadannan kwanaki 6, yawan mutanen da suka je wurin don yawon shakatawa ya kai kimanin dubu 100.(Lami)