Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-30 21:31:40    
An jaddada matsayin bin manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waja da kasar Sin ke dauka

cri

A ran 30 ga wata, kamfanin dillancin labaru na Xinhua na kasar Sin ya bayar da wani sharhin edita mai lakabi "tsayawa kan matsayin bin manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje domin sake neman samun babban cigaba" domin taya murnar cikon shekaru 59 da kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin.

Wannan sharhi ya bayyana cewa, a cikin shekaru 59 da suka gabata, a karkashin jagorantar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, jama'ar kasar Sin ta samu wata sabuwar hanyar da ke dacewa da tunanin gurguzu. Sun sanya kasar Sin wadda ke bin tsarin gurguzu, kuma ke neman zamanintar da kanta da neman hada kanta da sauran duniya, kuma ke neman wata kyakkyawar makoma ta kasance a gabashin duniya. Musamman a cikin shekaru 30 da suka gabata, bayan da aka aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, kasar Sin ta samu sauye-sauye mai ma'anar tarihi, zamantakewar jama'a ta kai matsakaicin karfi. Jimlar GDP ta duk kasar Sin ta kai matsayi na 4 a duk fadin duniya. Sha'anoni daban daban dukkansu sun samu babban cigaba gaba daya.

Wannan sharhi ya nuna cewa, an takaita fasahohi masu daraja da aka samu a cikin wadannan shekaru 30 da suka gabata bayan da aka aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, yana da muhimmiyar ma'ana ga kokarin kara raya sha'anin gurguzu da ke dacewa da halin musamman na kasar Sin a nan gaba. Jama'ar kasar Sin suna da imani cewa, ci gaba da 'yantar da tunani da tsayawa kan matsayin bin manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje da sa kaimi kan kokarin neman cigaba ta hanyar kimiyya da neman jituwa a zaman al'umam, tabbas ne za a samu babbar nasarar raya sha'anin gurguzu da ke dacewa da halin musamman na kasar Sin. (Sanusi Chen)