Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-30 20:20:10    
Shiyyoyin tattalin arziki na musamman da unguwannin raya tattalin arziki sun zama abin al'ajabi a kasar Sin

cri
Bisa labarin da aka bayar, an ce, a cikin shekaru 30 da suka gabata bayan da aka soma aiwatar da manufofin yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje a kasar Sin, shiyyoyin tattalin arziki na musamman da unguwannin raya tattalin arziki da ke matsayin kasar sun zama abin koyi a gida da wuraren da ke bayyana wa kasashen waje cigaban da kasar Sin ke samu. Sun kuma zama muhimman dakalin jawo jarin waje a kasar Sin. A waje daya kuma, sun ciyar da tattalin arziki na yankunan da suke ciki, kuma sun zama abin al'ajabi da ke bayyana yadda kasar Sin take bude kofarta ga kasashen waje.

A shekaru 1980 na karnin da ya gabata, an kafa shiyyoyin tattalin arziki na musamman guda 4, ciki har da shiyyar tattalin arziki ta musamman ta Shenzhen. Sannan a lokacin da ake shekaru 1990 na karnin da ya gabata, an kafa dimbin unguwannin raya tattalin arziki da ke matsayin kasa a larduna da manyan birane da yawa, kuma kasar Sin ta bude kofarta ga kasashen waje tun daga yankunan da ke kusa da teku zuwa yankunan da ke nesa da teku a kai a kai. Daga karshe dai, an bude kofarta daga dukkan fannoni baki daya. A cikin shekaru fiye da 20 da suka gabata, wadannan shiyyoyin tattalin arziki na musamman da unguwannin raya tattalin arziki na matsayin kasa sun samu sakamakon da ke jawo hankulan duniya sosai. Alal misali, birnin Shenzhen, wato wani karamin gari ne da ke kan iyakar kasa a da, yanzu ya zama wani babban birnin da yawan GDP nasa yana matsayi na 4 a cikin dukkan birane manya ko matsakaita na kasar Sin. A waje daya kuma, a shekara ta 2007, jimlar GDP na unguwannin raya tattalin arziki da suke matsayin kasa guda 50 ta kai kudin Sin yuan biliyan 1269.6. Bugu da kari kuma, sun riga sun zama muhimman sansanonin raya masana'antun mallakar fasahohin zamani. (Sanusi Chen)