Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-29 18:00:02    
Duniya ta kara fahimtar kasar Sin ta hanyar shiyar wasannin Olympics na Beijing, a cewar Hu Jintao

cri

Shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya bayyana cewa, gasar wasannin Olympics ta Beijing da kuma gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing sun sa jama'ar kasashe daban daban su taru a birnin Beijing a karkashin tutar Olympics mai zobba biyar, wadanda suka zama gagarumin biki wajen inganta cudanya a tsakanin jama'a na kasa da kasa da fahimtar juna da kuma zumuncin da ke tsakaninsu, ta haka duniya ta kara fahimtar kasar Sin, kuma kasar Sin ta kara fahimtar duniya.

Shugaba Hu Jintao ya fadi haka ne a gun babban taron yin yabo ga kungiyoyi da mutanen da suka bayar da gudummowa ga wasannin Olympics da wasannin Olympics na nakasassu na Beijing da aka shirya a ran 29 ga wata a Beijing.

Kuma shugaba Hu ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da daga tutar zaman lafiya da bunkasuwa da kuma hadin gwiwa, da bin makasudin manufofin harkokin waje na kasar Sin, wato kiyaye zaman lafiyar duniya da kuma sa kaimi ga samun bunkasuwa gaba daya, da inganta fahimta da zumuncin da ke tsakaninta da jama'ar kasashe daban daban, da raya dangantakar hadin gwiwa ta aminci tare da kasa da kasa domin ciyar da sha'anin zaman lafiya da bunkasuwar dan Adam zuwa gaba.(Kande Gao)