Yau 27 ga wata da yamma, da misalin karfe 4 da minti 58, dan sama-jannati na kasar Sin, Mr.Zhai Zhigang ya kammala ayyukan da ya gudanar a waje da kumbo, kuma ya koma cikin kumbo daga sararin samaniya, wannan kuma ya nuna cewa, karo na farko ne dan sama-jannati na kasar Sin ya cimma nasarar gudanar da harkoki a waje da kumbo.
Kafin ya koma cikin kumbo, Zhai Zhigang yi minti kimanin 20 yana gudanar da ayyuka a waje da kumbo cikin suturar musamman da Sin ta kirkiro da kanta, kuma ya karbi samfuran gwaje-gwaje da aka sanya a waje da kumbo.
Daga bisani, shugaban kasar Sin, Mr.Hu Jintao ya yi magana da 'yan sama-jannati da ke cikin kumbo, inda ya taya su murnar samun nasarar gudanar da ayyukansu a waje da kumbo. Ya kuma yi nuni da cewa, gudanar da ayyuka a waje da kumbo da 'yan sama-jannati suka yi cikin nasara ya nuna cewa, Sin ta sami babban cigaba a wajen zirga-zirgar kumbunan da ke dauke da mutane a sararin samaniya. Ya sa kaimi ga 'yan sama-jannati da su ci gaba da kokari, su kammala sauran ayyuka yadda ya kamata.
A ran nan da dare, kumbon ya kuma saki wani karamin tauraron dan Adam da zai yi masa rakiya. An ce, wannan karamin tauraron dan Adam zai dauki hotunan kumbon.(Lubabatu)
|