Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-27 17:03:05    
(Sabunta) Kumbo kirar "Shenzhou-7 " yana aikin yadda ya kamata

cri
A safiyar yau, manema labaru sun sami labarin daga cibiyar kula da sararin samaniya ta Beijing cewa, bisa rahoton duddubawar lafiyar jiki na karo na uku da aka yi wa 'yan sama-jannati, an ce, 'yan sama-jannati Zhai Zhigang da Liu Mingbo da Jing Haipeng suna da koshin lafiya. Ya zuwa karfe 10 da minti 47, kumbo "Shenzhou-7" ya riga ya zagaya duniya har sau 26 kamar yadda aka tsara, kuma ya yi tafiya har awoyi 37, yanzu kumbo "ShenZhou-7" yana aikin yadda ya kamata.

A wannan rana da safe, banyan da 'yan sama-jannati su uku sun karya kumallo a sararin samaniya, kuma sun taimaka wa juna wajen duddubawar lafiyar jikinsu. Daga bisani kuma, 'yan sama-jannati Zhai Zhigang da Liu Mingbo sun koma bangaren tafiya bisa hanyar zagaya duniya, kuma sun fara gudanar da ayyukan share fagen wajen yin tafiya a waje da kumbo. Kuma a wancan lokaci, ya kamata su kawar da dukkan kayayyakin da za su iya kawo matsala ga rage matsin iska daga bangaren da za a dawo da shi kasa, kuma sun duba nau'rar sarrafa bangaren kumbo tafiya bisa hanyar zagayen duniya, kuma sun yi Chaji ga tufafinsu.

Ran 27 ga watan, da karfe 1 da minti 33 da yamma, kumbo "ShenZhou-7" ya rufe kofar bangaren tafiya bisa hanyar zagaya duniya, 'yan sama-jannati sun fara gudanar da ayyukan yin tafiya a sararin samaniya. Hedkwatar ba da umurni wajen kula da tafiyar kumbo "ShenZhou-7 " ta tsaida umurni cewar, Zhai Zhigang zai zama 'dan sama-jannati da zai yi tafiya a waje da kumbo.(Bako)