Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-27 17:01:39    
Kumbo kirar "Shenzhou-7" yana aiki yadda ya kamata

cri
Ran 26 ga watan, da karfe 10 da minti 10 da yamma, agogon Beijing, 'yan sama-jannati na "Shenzhou-7" Zhai Zhigang da Liu Mingbo sun yi aikin horaswa a zauren kumbo.

A farko dai, Zhai Zhigang da Liu Mingbo sun yi aikin bincike kuma sun harhada tufafinsu da za su sanya a waje da kumbo, daga bisani kuma, sun sanya tufafinsu, kuma sun fara duba nau'rar sarrafa injin harhada da tufafinsu tare da kumbo da jarrabawarsu, haka kuma sun fara gudanar da aikin horaswa wajen yin tafiya.

Dukkan ayyukan da suka yi a cikin kumbo ya kai mitoci 100.Haka kuma za su kidaya tasirin da ayyukan 'yan sama-jannati suka kawo wajen tafiyar kumbo, don bayar da muhimmin adadi ga kyautata hanyar kumbo.

A cikin wannan lokaci, dan sama-jannati Jing Haipeng yana sa ido a kan tafiyar kumbo kuma ya bayar da rahoto ga cibiyar da ke kasa.

Babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'yyar kwaminis ta kasar Sin kuma shugaban kasar Sin, kuma shugaban kwamitin soja na tsakiya Mr. Hu Jintao ya karfafa kwarin gwiwa ga kowa da kowa don ba da tabbaci ga gudanar da ayyukan harbar kumbo Shenzhou-7 cikin nasara da ingiza sana'ar harbar kumbo mai dauke da 'yan sama-jannati gaba da kara bayar da sabuwar gudummawa gare su.(Bako)