Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-26 21:58:54    
Shugaban kasar Sin ya sa kaimi ga masu aikin sararin samaniya da su kara ba da taimako ga cigaban harkokin sararin samaniya na kasar Sin

cri
A ran 26 ga wata, a cibiyar harba taurarin dan Adam da ke garin Jiuquan na kasar Sin, shugaban kasar Sin, Mr.Hu Jintao ya gana da wakilan bangarorin nazarin kumbo kirar "Shenzhou-7" da ke dauke da mutane, kuma ya sa musu kaimi da su kara ba da taimako wajen tabbatar da samun cikakkiyar nasarar gudanar da kumbon da kuma dinga bunkasa harkokin zirga-zirgar kumbunan da ke dauke da mutane a sararin samaniya.

Mr.Hu Jintao ya ce, a ran 25 ga wata da dare, an harba kumbo kirar "Shenzhou-7" lami lafiya, kuma yanzu kumbon na tafiya kamar yadda aka shirya. Ya ce, a cikin shekaru 16 da Sin ke gudanar da shirin harba kumbunan da ke dauke da mutane, ta cimma manyan nasarori, har ta cimma mataki na biyu daga cikin matakai uku da aka tsara. Ya yi fatan masu aikin harkokin sararin samaniya za su cigaba da kokari, don kara ba da taimako ga bunkasuwar harkokin zirga-zirgar kumbunan da ke dauke da mutane a sararin samaniya.(Lubabatu)