Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-26 16:38:17    
Kafofin watsa labaru na Hongkong da Macao sun dora muhimmanci kan harba kumbo kirar "Shenzhou-7" mai dauke da mutane

cri

Yau rana ce ta biyu bayan da aka samu nasarar harba kumbo kirar "Shenzhou-7" mai dauke da mutane, kafofin watsa labaru na Hongkong da Macao dukansu sun bayar da labaru kuma sun nuna babban yabo ga lamarin.

Jaridar Wenhui ta Hongkong ta gabatar da sharhi cewa, harba kumbo kirar "Shenzhou-7" mai dauke da mutane muhimmin aiki dake da tasiri sosai na kasar Sin wajen kimiyya da fasaha, kuma shi wani kyakkyawan sakamakon da jama'ar kasar Sin ta samu wajen kimiyya da fasaha. Jaridun Dagong da Xingdao na Hongkong sun bayar da sharhi cewa, samun nasarar harba wannan kumbo ya shelanta cewa, kimiyya da fasaha na zirga-zirgar sararin samaniya na kasar Sin sun samu babban cigaba, kuma abin da ya fi muhimmanci shi ne tafiyar 'yan sama-jannati a sararin samaniya. Idan 'yan sama-jannati za su iya tafiya a sararin samaniya, to, kasar Sin za ta nuna karfinta wajen kimiyya da fasaha da wadata da kwadago da kuma sauransu bayan wasannin Olympic na Beijing.

Jaridar Daily ta Macao da jaridar kasuwanci da jaridar haske na Hongkong da kuma sauran gidajen TV da na Rediyo su ma sun bayar da labari game da hakikanin hali na harba kumbo kirar "Shenzhou-7".(Lami)