Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-26 16:29:41    
(Sabunta)Kafofin watsa labaru na kasashen waje sun dora muhimmanci kan sabon cigaban zirga-zirgar sararin samaniya da kasar Sin ta samu

cri

An samu nasarar harba kumbo kirar "Shenzhou-7" mai dauke da mutane a ran 25 ga wata, kafofin watsa labaru na kasa da kasa sun bayar da rahotanni da yawa kan lamarin, suna ganin cewa, wannan ya nuna cwa, sha'anin zirga-zirgar sararin samaniya na kasar Sin ya samu sabon cigaba.

Gidajen TV da yawa wato BBC da CNN da iTele da kuma sauransu suna can suna watsa labaru kai tsaye kan harbar kumbo kirar "Shenzhou-7" mai dauke da mutane, kuma sun bayar da labaru game da jerin ayyukan harbar wannan kumbo a shirye-shiryen labaru a kan TV, wasunsu sun gayyaci manazarta don ba da sharhi. ITele ya bayyana a cikin shirinsa cewa, harbar kumbo kirar "Shenzhou-7" mai dauke da mutane ya zama wani muhimmin lokaci wajen tarihi, kuma babu aibi a cikin jerin ayyukansa, wannan ya nuna cewa, kasar Sin ta samu sabon cigaba a fannin zirga-zirgar sararin samaniya.

Kamfannonin watsa labaru na kasashen waje wato AP na kasar Amurka da Reuters na Ingila da AFP na kasar Faransa da kuma sauransu su ma sun ba da labari ga harbar kumbo kirar "Shenzhou-7" mai dauke da mutane. Kamfannin AFP ya ce, samun nasarar harbar kumbo kirar "Shenzhou-7" mai dauke da mutane da shirin tafiya a sararin samaniya za su taimakawa kasar Sin wajen kafa tashar sararin samaniya da yin nazari kan duniyar wata. Gidan rediyon kasar Poland ya bayyana a cikin shirinsa na harbar kumbo kirar "Shenzhou-7" cewa, bayan da aka samu nasarar kira wasannin Olympic na Beijing, kasar Sin za ta sake samun nasarar wannan sabon aiki.

Jaridun kasashen waje su ma sun bayar da labaru da yawa kan harbar kumbo kirar "Shenzhou-7". Muhimman tashoshin Internet da yawa na wasu kasashe su ma sun gabatar hakikanan labaru game da wannan kumbo tare da hotuna da dama Dadin dadawa, kafofin watsa labaru na kasashen waje sun yi tsokaci kan ma'anar harbar wannan kumbo da tafiya a sararin samaniya sau na farko da kasar Sin ta yi.

Haka kuma, wani bayanin da shafin Internet na BBC ya gabatar ya ce, wannan lamari ya bayyana mana cewa, karfi da fasaha na kasar Sin wajen zirga-zirgar sararin samaniya sun samu bunkasuwa, amma idan kasar Sin tana son ta kai matsayin kasashen Amurka da Jamus, za ta bukaci cigaba da yin kokari.(Lami)