
A ran 25 ga watan da dare, babban kwamanda na ayyukan harbar kumbo mai dauke da mutane na kasar Sin Chang Wanquan ya ba da sanarwa a cibiyar harbar kumbo ta Jiuquan cewa, an samu nasarar harbar kumbo kirar "Shenzhou-7" mai dauke da mutane, kuma ya riga ya shiga hanyarsa domin aiwatar da ayyukan kumbo mai dauke da mutane a karo na uku.
Shugaban kasar Sin Hu Jintao ya kalli duk ayyukan harbar kumbo a cibiyar harbar kumbo ta Jiuquan, kuma ya taya murnar nasarar da aka samu kan harbar kumbo. Ya bayyana cewa, aiwatar da ayyukan kumbo kirar "Shenzhou-7" mai dauke da mutane shi ne aikin yin binciken kimmiya mafi muhimmanci da zai kawo tasiri sosai a kasar Sin a shekarar nan, kuma alama ce dake nuna cewa wannan aikin harbar kumbo mai dauke da mutane ya samu nasara ta farko.
Da misalin karfe 4 da mintoci 4 da safe na yau, kumbo kirar "Shenzhou-7" mai dauke da mutane ya shiga hanyar zagaya duniya da tasowanta ya kai kilomita 343 daga kasa. 'yan sama jannati suna cikin koshin lafiya a fannonin zafin jiki da bugun jini da dai sauransu. (Asabe)
|