Ran 25 ga wata a birnin Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Liu Jianchao ya ce, ayyukan harba kumbo kirar "Shenzhou-7" wani muhimmin mataki ne na kasar Sin wajen binciken yin amfani da sararin samaniya cikin lumana.
A gun taron manema labaru da aka shirya a yau, Mr Liu ya ce:
Kasar Sin tana tsayawa tsayin daka kan yin amfani da sararin samaniya cikin lumana. Babban makasudi na ayyukan kumbo mai dauke da mutane na kasar Sin shi ne bincike da kuma yin amfani da sararin samaniya, domin raya tattalin arzikin kasar da dadin zaman walwala na jama'a. A cikin wannan karo, ayyukan harba kumbo kirar "Shenzhou-7" wani muhimmin mataki ne na kasar Sin wajen yin kokari domin bincike kan yin amfani da sararin samaniya cikin lumana.(Fatima)
|