Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-25 16:22:18    
'Yan sama-jannati na kasa da kasa sun yi fatan alheri ga kasar Sin yayin da za ta harbar kumbo kirar "Shenzhou-7" cikin nasara

cri
Yayin da ake shirin harba kumbo kirar "Shenzhou-7" a kasar Sin, 'yan sama-jannati na kasa da kasa sun nuna kyakkyawan fatan alherinsu ga takwarorinsu na kasar Sin da za ta harba kumbo mai dauke da 'yan sama-jannati cikin cikakkiyar nasara.

Dan sama-jannati na kasar Amurka, Jeffrey Hoffman mai shekaru 63 da haihuwa, wanda ya taba aiki a sararin samaniya fiye da sa'o'i 1000, ya yi fatan alheri ga takwarorinsa na kasar Sin cewa, yana fatan za su iya sauke nauyin da ke bisa wuyansu cikin nasara.

Mashahurin dan sama-jannati na kasar Amurka, wanda dan asalin kasar Sin ne, Edward Tsang Lu ya bayyana cewa, yana fatan za a iya harbar kumbo kirar "Shenzhou-7" cikin nasara. Haka kuma ya bayyana cewa, tafiya a kan sararin samaniya wani muhimmin aiki ne wajen bincike sararin samaniya, kuma zai kasance babban ci gaba da Sin ta samu wajen bincike sararin samaniya.

'Yar sama-jannati ta kasar Japan watau wadda ta taba gudanar da ayyuka a sararin samaniya, kuma mata ta farko da ta taba tafiya sau biyu a sararin samaniya Mukai Chiaki ta bayyana cewa, saurin bunkasuwar sha'anin sararin samaniya na kasar Sin ya baiwa mutane mamaki, ko da karo na 3 ne nan da Sin ta harba kumbo mai dauke da 'yan sama-jannati zuwa sararin samaniya, amma ga shi tana shirya tafiya a sararin samaniya. Tana fatan Sin za ta cimma nasara.(Bako)