Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-24 16:54:56    
Kasar Sin za ta harba kumbo mai lambar bakwai samfurin 'shenzhou' da ke dauke da 'yan sama jannati a ran 25 ga wata da dare

cri

A ran 24 ga wata, a cibiyar harba tauraron dan Adam ta Jiuquan Mr.Wang Zhaoyao, kakakin ayyukan tafiyar kumbon da ke dauke da 'yan sama jannati ya nuna cewa, kasar Sin za ta harbar kumbo mai lambar bakwai samfurin 'shenzhou' da ke dauke da 'yan sama jannati a daren ran 25 ga wata.

A gun taron manema labaru da aka yi a ran nan, ya nuna cewa, ofishin ba da jagoranci kan harkokin kumbo mai lambar bakwai samfurin 'shenzhou' ya yanke shawarar za a harbar kumbo mai lambar bakwai samfurin 'shenzhou' tun daga karfe 9 da minti 7 zuwa karfe 10 da minti 27 da dare. Muhimmin nufin aikin shi ne gudanar da aikin fita daga cikin kumbo a karo na farko da 'yan sama jannati na kasar Sin za su yi bisa shirin da aka tsayar, kuma kara samun ilmin fita daga cikin kumbo. 'Yan sama jannati guda 3 sun zama rukunin zirga-zirga a sararin samaniya don gudanar da aikin.

Wang Zhaoyao ya ce, a halin yanzu, an kammala atisayen daga duk fannoni wajen dukan tsarin gudanar da aikin, kuma an gudanar da ayyukan shirin daban daban kafin harbar kumbon.(Zainab)