Bisa "shirin sake farfadowa daga manyan fannoni bayan mummunan bala'in girgizar kasa da ya fadawa Wenchuan" da shafin Internet na gwamnatin kasar Sin ya bullo jiya 23 ga wata, an ce, a cikin nan da shekaru 3 masu zuwa, Sin na shirin yin amfani da kudin Sin Yuan biliyan 1000, domin kammala aikin sake farfado da yankunan da suka fi fama da bala'in girgizar kasa a lardunan Sichuan, da Gansu, da Shanxi, ta yadda sharadin zaman rayuwar jama'a da tattalin arziki da zamantakewar al'umma na wadannan yankuna za su sami kyautatuwa kamar yadda suke a gabannin faruwar bala'in girgizar kasa. Bugu da kari kuma, Sin na shirin dukufa ka'in da na'in wajen sake farfado da yankunan da bala'in girgizar kasa ya galabaita har su zama sabbin gidaje, inda mutane za su iya jin dadin zamansu da gudanar da ayyuka cikin wani yanayi mai kyau.
Babban burin shirin shi ne, na farko, a kammala ayyukan sake farfado da matsugunai a birane da kauyuka, ta yadda mutanen da bala'in girgizar kasa ya ritsa da su za su iya jin dadin zamansu a sabon gida ba tare da kashe kudi da yawa ba. Na biyu, a cikin duk wani gida, akalla dai mutum daya zai iya samun gurbin aikin yi, yawan kudin shiga da kowane mazaunin birane da kauyuka ya samu zai zarce yawan kudin shiga da ya samu a gabannin bala'in girgizar kasa. Na uku wato na karshe shi ne, mutanen da bala'in girgizar kasa ya ritsa da su za su ji dadin tsarin bada tabbaci ga zaman rayuwarsu, da dai sauran muhimman hidimomi, ciki har da ayyukan bada ilimin tilas, da kiwon lafiya, da samun aikin jinya, da wasannin motsa jiki, da dai sauransu.(Murtala)
|