Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-23 16:44:36    
An kammala bincike hadin gwiwa ga roka da kumbo mai lambar bakwai samfurin 'shenzhou' a karo na karshe

cri
A ran 23 ga wata da safe, a filin harba kumbo mai lambar bakwai samfurin 'shenzhou', an gudanar da bincike cikin hadin gwiwa a tsakanin roka da kumbo da filin harba kumbo, wannan ya alamanta cewa, ya riga ya shiga lokacin kusan harba kumbo.

A ranar da karfe 9 da safe, akwai kwararru da ma'aikatan bangarori daban daban da yawa da ke zaune a ofishin ba da jagoranci na cibiyar harba tauraron 'dan Adam ta Jiuquan. Bisa labarin da babban jagoran tsarin harba kumbo Mr.Cui Jijun ya bayar, ya ce, a kwanan baya, bayan an yi jigilar kumbo daga filin fasaha ta hanyar jirgin kasa da ke da tsawon mita 1500, halin da kumbo ke ciki ya riga ya canza, dole ne a gudanar da bincike cikin hadin gwiwa ga kumbo.

A ran nan da karfe 10 da rabi da safe, an gama gudanar da bincike lami lafiya. Bisa sakamakon binciken, an shiga lokacin jiran harba kumbo.(Abubakar)