Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-23 15:46:01    
(Sabunta)Gagarumin bikin taya murnar cika shekaru 50 da kafa jihar Ningxia ta kabilar Hui mai cin gashin kanta a Yinchuan

cri

Da safiyar yau 23 ga wata din nan ne, aka yi gagarumin bikin taya murnar cika shekaru 50 da kafa jihar Ningxia ta kabilar Hui mai ikon tafiyar da harkokin kanta a hedkwatar jihar wato birnin Yinchuan, wanda ya samu halartar kungiyar wakilan kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin dake karkashin jagorancin He Guoqiang, zaunannen memban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar.

A cikin wani muhimmin jawabin da ya yi a wajen taron, He ya bayyana cewar, burin samun bunkasuwa da zaman karko mai dorewa da jihar Ningxia ke kokarin neman cimmawa yana bukatar a tsaya tsayin daka kan manufar cin gashin kai a yankunan kananan kabilu da cigaba da kyautata shi, da karfafawa da raya dangantakar hadin-kai mai jituwa irin ta gurguzu cikin halin daidaici tsakanin kabilu daban-daban ba tare da kakkautawa ba. Bugu da kari kuma, ya zama tilas Ningxia ta nace ga maida aikin habaka tattalin arzikinta a gaba da kome, da daukaka cigaban yunkurin bude kofa ga kasashen ketare da yin gyare-gyare, da sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'umma cikin halin daidaici, tare kuma da inganta kwarewarta wajen raya kanta.

A ranar kuma, kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, da kwamitin din-din-din na majalisar wakilan jama'ar kasar, da majalisar gudanarwa ta kasar, da majalisar bada shawara kan harkokin siyasa ta kasar, tare kuma da kwamitin soja na tsakiya sun aika da sakon taya murna, inda suka taya murnar cika shekaru 50 da kafa jihar Ningxia ta kabilar Hui mai ikon tafiyar da harkokin kanta. Sakon ya ce, rike da zarafi domin daukaka cigaban tattalin arziki da zamantakewar al'umma ta Ningxia, da karfafawa da raya dangantakar hadin-kai mai jituwa irin ta gurguzu cikin halin daidaici tsakanin kabilu daban-daban shi ne babbar moriyar jama'ar kabilu daban-daban a Ningxia, kuma shi ne babban burin da kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da jama'ar kabilu daban-daban na dukkan kasar ke neman cimmawa. Jam'iyyar kwaminis ta kasar, da dukkan kasar Sin za su nuna cikakken goyon-baya ga harkokin raya Ningxia kamar yadda suke yi a lokacin da, ta yadda za'a samar da kyakkyawan zarafi ga bunkasa Ningxia da kyau kuma cikin sauri.(Murtala)