A ranar 22 ga wata, majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta fitar da bayanin halin da ake ciki wajen ayyukan yaki da bala'in girgizar kasa da ya auku a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan, da ayyukan ceto. Ya zuwa ranar 22 ga wata da karfe 12, gwamnatoci na matakai daban daban sun bayar da kudin Sin RMB fiye da biliyan 76.8 kan ayyukan yaki da bala'in da na ceto.
An ce, ya zuwa ranar 22 ga wata da karfe 12, mutane 69,227 sun rasa rayukansu a sakamakon girgizar kasa ta gundumar Wenchuan, yayin da mutane 374,643 suka ji rauni, bayan haka kuma, mutane 17,923 suka bace.
Bugu da kari kuma, hukumomin da abin ya shafa na kasar Sin sun samu taimakon kudi da na kayayyaki masu darajar kudin Sin RMB kusan biliyan 59.5 daga bangarori daban daban na gida da waje. (Bilkisu)
|