Ran 20 ga wata da misalin karfe 3 da minti 15 na yamma, kumbo mai ratsa sararin samaniya kuma mai daukar mutane kirar Shenzhou-7 da roka kirar Changzheng-2F sun isa wurin harba a tsaye yadda ya kamata, wannan ya almanta cewa, an riga an shiga mataki na karshe na share fagen harba kumbo mai daukar mutane kirar Shenzhou-7.
Yanzu, an riga an cika kumbon da abun farfela. Bayan da babbar hedkwatar ba da umurni a kan harba kumbon ta tsai da kudurin cika rokar da abun farfela, za a harba kumbon in akwai dama.
Kafin wannan kuma, kakakin kula da aikin harba kumbo mai ratsa sararin samaniya kuma mai daukar mutane na kasar Sin ya sanar da cewa, za a harba kumbo mai ratsa sararin samaniya kuma mai daukar mutane kirar Shenzhou-7 a ran 25 zuwa ran 30 ga wata in akwai dama. A lokacin can, 'yan sama-jannati 3 za su yi aiki a cikin kumbon. Daya daga cikin muhimman ayyuka na kumbo mai daukar mutane kirar Shenzhou-7 shi ne tabbatar da ganin wani dan sama-jannati ya fita daga kumbon.(Tasallah)
|