Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-20 16:37:20    
Za a yi jigilar kumbo kirar Shenzhou-7 zuwa wurin harba

cri
Ran 19 ga wata, wani jami'in cibiyar harba tauraron dan Adam da ke Jiuquan na lardin Gansu a arewa maso yammacin kasar Sin ya bayyana cewa, a ran 18 ga wata, an kammala hada kumbo mai ratsa sararin samaniya kuma mai daukar mutane kirar Shenzhou-7 da roka kirar Changzheng-2F, nan gaba kadan za a yi jigilar shi zuwa wurin harba.

Wannan jami'i ya kara da cewa, bayan da aka ajiye kumbon da rokar a cibiyar, ma'aikatan manyan tsare-tsaren kumbo mai ratsa sararin samaniya kuma mai daukar mutane sun sha yin gwaje-gwaje tare, kuma halin da kumbon da rokar suke ciki yana da kyau, ana gudanar da ayyukan share fage yadda ya kamata.

Za a harba kumbo mai ratsa sararin samaniya kuma mai daukar mutane kirar Shenzhou-7 a ran 25 zuwa 30 ga wata in akwai dama.(Tasallah)