Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-20 16:19:17    
Kasar Sin ta gode wa sauran kasashen duniya wajen shirya wasannin Olympic na Beijing cikin nasara

cri
A ran 19 ga wata da dare a nan birnin Beijing, an shirya liyafar nuna godiya domin gasar wasannin Olympic ta Beijing da gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing. Mr. Xi Jinping, mataimakin shugaban kasar Sin ya halarci wannan liyafa, kuma ya bayar da wani jawabi, inda ya nuna godiya ga wadanda suka bayar da gudummowa wajen samun cikakkiyar nasarar gasar wasannin Olympic ta Beijing da gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing. Ya kuma jaddada cewa, kasar Sin za ta hada kan jama'ar sauran kasashen duniya wajen yin kokarin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa da neman raya wata duniya mai jituwa kuma mai cigaba.

Ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin da kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing sun shirya wannan liyafa tare domin nuna godiya ga goyon bayan da sauran kasashen duniya da kungiyoyin duniya suka nuna wa gasar wasannin Olympic ta Beijing da gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing. An gayyaci baki kusan dari 4 da suka hada da jakadun kasashen waje da wakilan kungiyoyin kasa da kasa da ke nan kasar Sin da su halarci wannan liyafa.

A gun liyafar, Mr. Xi ya ce, gasar wasannin Olympic ta Beijing da gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing dandamali ne inda 'yan wasa na kasashe da yankuna daban daban suka cimma burinsu. Su kuma dakali ne da ke sada zumunta da fahimtar juna a tsakanin jama'ar al'ummomi daban daban. (Sanusi Chen)