Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-18 14:33:05    
Kasar Sin za ta yawaita yin amfanin da sakamakon da aka samu a gun gasar wasannin Olympic wajen kimiyya da fasaha

cri
Ran 17 ga watan, a gun taron shekara-shekara na karo na 10 da aka shirya a birnin Zhengzhou wajen kimiyya da fasaha, ministan kimiyya da fasaha na kasar Sin Wan Gang ya bayyana cewa, Sin za ta ci gaba da yawaita yin amfani da sakamakon da aka samu a gun gasar wasannin Olympic wajen kimiyya da fasahar bayan wasannin Olympic.

Wang Gang ya bayyana cewa, bayan da Sin ta tantance aikinsu a gun gasar wasannin Olympic, Sin za ta kara kera motocin da suke yin amfani da sabbabin makamashi. Haka kuma fasahar sadarwa ta tafi da gidanka ta 3 za ta ci gaba da bunkasa sana'ar sadarwa. Fasahar tsarin sarrafa wutar lantarki ta makamashin hasken rana da semiconductor za su ci gaba da samun bunkasuwa. Haka kuma za a ci gaba da yin amfani da fasahohi wajen kiyaye muhalli da yin tsimin makamashin da rage yawan abubuwa masu gurbata yanayi. Haka kuma karafen da aka yi amfani da su wajen gina dakuna da filayen gasar wasannin Olympic, za a kara yin amfani da shi wajen tsara gine-ginen jama'a.(Bako)