Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-17 21:53:40    
An rufe gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing

cri

Yau wato ran 17 ga wata da dare, an rufe gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing ta shekara ta 2008, kuma Philip Craven, shugaban kwamitin wasannin Olympics na nakasassu na duniya ya nuna yabo kan cewa, gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta wannan karo ita ce gasar wasannin Olympics ta nakasassu mafi kyau a tarihi. Kuma ya yi kira ga dukkan 'yan wasa da malaman horaswa da kuma jami'ai da su yada ruhin wasannin motsa jiki na musamman na wannan gasar zuwa wurare daban daban, ta yadda za a iya kara kwarin gwiwar yawan mutane wajen sa hannu a cikin wasanni da samun abokai da kuma kunna wutar da ke cikin zukatansu.

Shugaba Hu Jintao na kasar Sin da shugabanni da wakilan sarakuna fiye da 20 na kasashen wajen sun halarci bikin rufe gasar na ranar Laraba da dare.

Bisa kidayar da bangaren gwamnati ya bayar, an ce, gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta wannan karo ta karya bajimta a fannonin yawan kasashe da yankunan da suka sa hannu a cikin gasar, da yawan matsayin bajimta na duniya da aka karya, da yawan kafofin watsa labarai da suka sa hannu a cikin gasar, da kuma yawan 'yan kallon wasannin. Haka kuma bisa kididdigar da aka yi, an ce, kungiyoyin 'yan wasa da suka zo daga kasashe da yankuna 147 sun shiga gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta wannan karo, kuma 'yan kallo kimanin miliyan 1.1 sun kalli gasanni kai tsaye.(Kande Gao)