Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-16 21:34:27    
Gasar Olympic ta nakasassu ta Beijing ta ba da kayayyakin tarihi masu daraja ga duniya

cri

Ran 16 ga wata, yayin da Mr. Antonio da Luz babban sakataren kwamitin wasannin Olympic na nakasassu na kasar Angola ke ganawa da wakilinmu ya nuna cewa, gasar Olympic ta nakasassu ta Beijing wani taro mai inganci sosai, dole ne za ta ba da kayayyakin tarihi masu daraja ga kasashen duniya.

Wannan shi ne karo na hudu da Mr. Antonio ya halarci gasar Olympic ta nakasassu. Ya ce, bisa gasannin Olympic na nakasassu da suka yi a baya, 'yan wasa sun sami sakamako mai kyau sosai cikin gasar Olympic ta nakasassu ta Beijing, kuma sun karya bajimtar duniya da bajimtar gasar Olympic ta nakasassu da yawa. Yana ganin cewa, an sami hakan a sakamakon saurin bunkasuwar wasannin nakasassu na duniya.

Mr. Antonio ya ce, an gudanar da ayyukan shirya gasar Olympic ta nakasassu ta Beijing maras aibi, ana kula da 'yan wasa sosai yayin da ake yin gasanni.