Ran 14 ga wata da dare, 'dan wasa Henry Kiporono Kirwa na kasar Kenya ya samu lambar zinariya cikin gasar maza ta gudun mita dubu 10 ta ajin T12 da mintoci 31 da dakika 42.97, kuma ya karya matsayin bajimtar gasar Olympic ta nakasassu. Wannan lambar zinariya ta uku da ya samu ga kungiyar wakilan kasar Kenya.
Yayin da yake ganawa da wakilinmu, Mr. Kirwa ya nuna cewa, yana jin farin ciki sosai saboda ya samu lambar zinariya ga kasarsa Kenya. A sa'i daya kuma, ya nuna cewa, ya samu kyakkyawan sakamakon iri haka saboda kokarin ya yi. Ya ce, kafin an fara yin gasa, kafarsa ta dama ta jikkata, likita ya ba da agaji mai gaggawa, duk da haka, yana sha zafi yayin da ake yin gasa, amma yana jin farin ciki saboda ya samu lambar zinariya a karshe.
|