Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-14 16:56:51    
Gasannin Olympic na Beijing biyu dukkansu gasannin Olympic ne masu kayatarwa, a cewar Zainal Abu Zarin

cri
A ran 13 ga wata, lokacin da yake ganawa da manema labaru na kasar Sin, Mr. Dato Zainal Abu Zarin, shugaban kwamitin wasannin Olympic na nakasassu na Asiya ya bayyana cewa, gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing gasar wasannin Olympic ta nakasassu ce mafi kyau a tarihi. Kasar Sin ta cika alkawarinta na shirya gasannin Olympic biyu masu kayatarwa.

Mr. Abu Zarin ya ce, lokacin da ake yin gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing, ya gana da 'yan wasa da jami'ai da yawa a gun gasanni da unguwar 'yan wasa, har yanzu bai ji ko wani mutum ya zargi wannan gasar wasannin Olympic ta nakasassu ba. Ko shakka babu, gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing gasar wasannin Olympic ce mafi kyau a tarihi, kowa yana jin dadinta.

A matsayin shugaban kwamitin kula da wasannin Olympic na nakasassu na Asiya, Mr. Abu Zarin yana farin ciki sosai sabo da an shirya wannan gasar wasannin Olympic ta nakasassu a Asiya. Ya kuma yaba wa mazauna Beijing da su yi abubuwan koyi ga jama'ar sauran yankunan Asiya. Birnin Beijing ya yi kokari sosai wajen shirya gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing kamar yadda ta shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing. Ya kara da cewa, wannan gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta sa kaimi ga kokarin raya wasannin motsa jiki na nakasassu a Asiya. Kuma zai samu sauki wajen yin aikinsa. Mr. Abu Zarin ya ce, yana jin alfahari sosai ga gasar wasannin Olympic ta nakasassu. (Sanusi Chen)