
Ran 13 ga wata, ana ci gaba da gasar wasannin Olympic ta nakasassu a nan Beijing, a cikin gasar daukar karafa da 'yan wasa maza nakasassu, wadanda ajin nauyinsu bai wuce kilo 67.5 ba, 'yan wasa daga kasashen Masar da Iran da kuma Sin sun zama na farko da na biyu da kuma na uku.

Dan wasa Zakari Adamou, wanda dan wasa daya tak da kasar Nijer ta aika da shi zuwa nan Beijing ya zama na 13, bai sami lambar yabo ba, amma ya sami maki mafi kyau bayan da ya fara yin wasan daukar nauyi.(Tasallah)
|