Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-13 17:26:52    
Wasu shugabannin kasashen ketare za su kawo ziyara a nan kasar Sin, kuma za su halarci bikin rufe wasannin Olympics na nakasassu

cri
Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin madam Jiang Yu ta bayar da sanarwa a ranar 13 ga wata cewa, wasu shugabannin kasashen katera za su kawo ziyara a nan kasar Sin a 'yan kwanaki masu zuwa, bayan haka kuma za su halarci bikin rufe wasannin Olympics na nakasassu na Beijing.

Bisa gayyatar da gwamnatin kasar Sin ta yi, shugaba Joao Bernardo Vieira na kasar Guinea Bissau, da firayin minista Seini Oumarou na kasar Nijer za su kawo ziyara a kasar Sin tun daga ranar 16 ga wata, bugu da kari kuma, shugabanni daga kasashen Jordan, da Bengal, da Samoa, da Turkmenistan, da kuma Tonga za su kawo ziyara a nan kasar Sin, kuma dukkansu za su halarci bikin rufe wasannin Olympics na nakasassu na Beijing.

Har wa yau kuma, shugaba Vieira na kasar Guinea Bissau ya bayyana a kwanan baya a Bissau cewa, halartar bikin rufe taron wasannin Olympics na nakasassu na Beijing, da kuma yin ziyarar aiki a kasar Sin da zai yi a 'yan kwanaki masu zuwa, wannan dai ya ba shi da iyalansa dama wajen dinke bakin ciki da suka yi saboda rashin halartar bikin bude wasannin Olympics na Beijing.

Shugaba Vieira ya ce, ziyarar da zai yi a kasar Sin ta nuna cewa, an kai dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi da ba a taba gani ba. (Bilkisu)