Mako daya bayan da aka fara wasannin Olympic na nakasassu a nan birnin Beijing, jami'an wasu kasashe sun nuna babban yabo a kansa, kuma sun ce, wasannin Olympic na nakasassu na da kayatarwa daidai kamar yadda aka shirya wasannin Olympic.
A ran 11 ga wata, a gaban kafofin yada labarai ne, Sene Hagne, shugaban hadaddiyar kungiyar nakasassu ta Senegal ya ce, Sin ta cika alkawarinta, kuma wasannin Olympic na nakasassu yana da kayatarwa daidai kamar yadda Beijing ta gudanar da wasannin Olympic, kuma ya burge duniya. Beijing ya samar da dandali mafi kyau na yin mu'amala tsakanin kungiyoyin nakasassu da kuma 'yan wasa nakasassu na kasashe daban daban.
Bayan haka, a yayin da Jan Figel, wakilin tarayyar Turai da ke kula da harkokin ilmi da horaswa da kasancewar al'adu da kuma harsuna daban daban, ke hira da manema labarai na kasar Sin, ya ce, wasannin Olympic na nakasassu na Beijing ya nuna al'adun dan Adam da kuma hadin kan al'umma, ya kuma nuna yabo ga yadda kwamitin wasannin Olympic na nakasassu na Beijing ke gudanar da aikinsa.(Lubabatu)
|