|
|
 |
 |
| Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
| (GMT+08:00)
2008-09-12 21:43:59
|
|
Sin za ta tabbatar da ingancin abinci a zangon karshe na wasannin Olympic na nakasassu
cri
|
Yau babbar hukumar gudanar da harkokin masana'antu da kasuwanni ta kasar Sin ta bayar da sanarwar gaggawa, inda ta nemi wurare daban daban da su kara aiwatar da dokoki a kasuwanni, don tabbatar da ingancin abinci a wajen saye da sayarwa a zangon karshe na wasannin Olympic na nakasassu.
Hukumar dai ta nemi wurare daban daban da su kara sa ido a kan manasana'antun da ke samar da abinci ga wasannin Olympic na nakasassu da kuma kantuna a kasuwannin da ke sayar da abincin, a kara sa ido a kan ingancin abinci da kuma kara binciken kasuwannin sayar da abinci, kuma a janye abincin da ba su da inganci nan da nan idan an gano su.(Lubabatu)
|
|
|