Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-12 16:53:29    
Kwamitin shirya wasannin Olympic na nakasassu na duniya ya nuna babban yabo ga ayyukan share fagen wasannon Olympic na nakasassu na Beijing

cri

Aran 12 ga watan, wani jami'in kwamitin shirya wasannin Olympic na nakasassu na duniya ya bayyana cewa, kwamitin shirya wasannin Olympic na nakasassu na duniya ya nuna babban yabo ga ayyukan share fagen wasannon Olympic na nakasassu na Beijing.

A gun taron watsa labarum da cibiyar watsa labaru na wasannin Olympic na nakasassu na Beijing ta yi a ran nan a nan birnin Beijing, direktan hukumar wasannin motsa jiki na kwamitin shirya wasannin Olympic na nakasassu na duniya David Grevemberg ya bayyana cewa, tun daga suka iso babban ginin jiran jiragen sama mai lamba 3 a filin jiragen sama na Beijing, suka zauna a kauyen wasannin Olympic na nakasassu, suka zo filaye wasannin Olympic, da yin yawo a nan Beijing, suna iya zama da aiki lami lafiya, kuma 'yan wasa suna iya yin gasanni cikin filaye masu kyau. Suna jin dadi a kan wannan. Sabo da haka, kwamitin shirya wasannin Olympic na nakasassu na duniya suna nuna babban yabo ga wasannin Olympic na nakasassu na Beijing.

Bugu da kari, Mr. David Grevemberg ya bayyana cewa, gwamnatin birnin Beijing da gwamnatin tsakiya suna nuna goyon baya ga wasannin Olympic na nakasassu na Beijing, kuma aikin hadin gwiwa tsakanin gwamnatocin da kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing ya samu babbar nasara a tarihin wasannin Olympic na nakasassu.(Asabe)