Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-11 21:24:56    
'Yan kallo na kasar Sin sun nuna aminci da zafin nama

cri

A yayin da yake zantawa da wakilin Gidan Rediyon kasar Sin a yau ranar 11 ga wata, shugaban hukumar wasannin Olympics ta nakasassu ta kasar Kenya Mr. Douglas Sidialo ya bayyana cewa, a gun gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing, aminci da zafin nama da 'yan kallo na kasar Sin suka nuna sun burge shi sosai. Musamman ma 'yan kallo na kasar Sin ba su yi ihu na ba da kwarin gwiwa ga 'yan wasa na kasar Sin kawai ba, har ma sun yi wa 'yan wasa na sauran kasashe, Mr. Sidialo ya yaba wa hakan sosai da sosai.

Bayan da ya kalli gasannin daukar nauyi na maza, Mr. Sidialo ya ce, 'yan kallo na kasar Sin sun nuna aminci da al'adu da hadin kai ga duk duniya, sabo da haka ne, ya nuna godiya ga 'yan kallo da suka ba da kwarin gwiwa ga 'yan wasa na kasa da kasa, ayyukansu sun bayyana wa ma'anar wasannin Olympics ga jama'a.(Danladi)