A ran 10 ga wata, mataimakin shugaban hukumar binciken kudi ta kasar Sin Mr. Yu Xiaomin ya bayyana cewa, bayan aukuwar girgizar kasa a gundumar Wenchuan, mutane na fannoni daban daban sun bayar da taimakon kudi da kayayyakin agaji masu dimbin yawa domin taimakon jama'ar gundumar Wenchuan da girgizar kasa ta ratsa da su. Bayan da aka yi bincike, an gano cewa, an yi amfani da kudaden da kayayyakin agaji kamar yadda ya kamata, har yanzu babu matsala.
Lokacin da Mr. Yu Xiaomin ya yi tattaunawa da mutane ta hanyar Internet, ya bayyana cewa, ana binciken yadda aka yi amfani da kudaden da kayayyakin agaji da aka bayar, haka kuma ana binciken hanyoyin da aka yin amfani da su.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, an gano ayyuka 36 da aka aikata ba daidai ba ne, yanzu, an labtarwa mutane 21 da abin ya shafa bisa tsarin dokoki na JSK da na gwamnati. (Zubairu)
|