
A ran 10 ga wata, a birnin Beijing, Elynah Sifuna Shiveka, mai kula da sashen wasannin motsa jiki ta kamfanin KBC ta bayyana cewa, an karbi 'yan jarida da hannu bibbiyu da ba su hidima yadda suka bukata a wasannin Olympics na nakasassu na Beijing.


Yayin da Elynah Sifuna Shiveka, shugabar ma'aikatar motsa jiki ta kamfanin KBC ta yi hira da wakilin gidan rediyon kasar Sin a cibiyar watsa labaru ta wasannin Olympics na nakasassu na Beijing, ta bayyana cewa, birnin Beijing ya nuna fiffiko wajen karbar 'yan jarida a wasannin Olympics na nakasassu na Beijing, komai na tafiya daidai. Tsarin neman labarar gasanni yana da sauki sosai, kuma hanyoyin sadarwa na internet na da saukin bi, abincin da ake samarwa a kyauta a kowace rana na da dadin ci, 'yan jaridan kasa da kasa suna jin dadin aiki da zama a cikin wannan hali.(Zainab)
|