Yau 10 ga wata, firaministan kasar Sin, Mr.Wen Jiabao ya shugabanci taron majalisar gudanarwa, inda aka yi nazari a kan "ra'ayoyi game da zurfafa gyare-gyaren tsarin kiwon lafiya", kuma aka yanke shawarar sake neman shawarwari daga al'umma.
Ra'ayoyin dai sun gabatar da makasudin da za a cimmawa a wajen gyare-gyaren tsarin kiwon lafiya da kuma manufofi da matakai da za a dauka. Daga cikinsu, babban makasudin da za a cimmawa shi ne, ya zuwa shekarar 2020, a kafa tsarin kiwon lafiya da zai shafi mazaunan birane da kauyuka gaba daya, kuma a samar wa al'umma magunguna da jiyya mai inganci kuma cikin farashi mai sauki, ta yadda za a dinga inganta lafiyar jikin jama'a.(Lubabatu)
|