Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-10 20:36:41    
Mr. Craven ya ce, gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing ta fi kyau a tarihi

cri

Shugaban hukumar wasannin Olympics ta nakasassu ta duniya Mr. Philip Craven ya bayyana a ran 10 ga wata a Hongkong cewa, gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing ta fi kyau a tarihi, a matsayin birnin da ke ba da taimako wajen shirya gasannin tseren dawaki na nakasassu, Hongkong ya taka wata muhimmiyar rawa kamar birnin Beijing da ke daukar nauyin shirya gasannin da biranen Qingdao da dai sauran biranen da suke ba da taimako wajen shirya gannin Olympics na nakasassu.

Gwamnan yankin musamman na Hongkong Mr. Donald Tsang ya kira liyafar rana ga Mr. Craven da uwar gidansa. Bayan da ya yi rangadi a filayen gannin tseren dawaki na Olympics a Hongkong, Mr. Craven ya yaba wa filayen sosai da sosai. Mr. Donald Tsang ya nuna godiya ga bangarori daban daban na Hongkong wajen hada kansu domin shirya gasar wasannin Olympics ta nakasassu yadda ya kamata.(Danladi)