A kwanakin nan, akwai wadansu shugabannin kasashen waje da suka taya murna ga birnin Beijing bisa cimma nasarar shirya gasar wasannin Olympic ta hanyar waya ko kuma aika sakoni.
Shugaban kasar Laos Mr Choummaly Sayasone yana mai ra'ayi cewa, gasar wasannin Olympic na Beijing ta sa kasar Sin ta samu suna a duk duniya, kuma ta sake bayyana wa duniya cewa jama'ar kasar Sin suna cikin hadin kai sosai.
Shugaban kasar Mexico Mr. Felipe Calderon ya bayyana cewa, kyakkyawar aikin shirya gasar wasannin Olympic na Beijing ya nuna cewa kasar Sin tana da daddaden tarihin al'adu, kuma ya bayyana halin mai armashi da kasar Sin ke ciki da kuma makomarta mai haske.
Babbar gwamnar kasar Canada madam Michaelle Jean ta bayyana cewa, gasar wasannin Olympic na Beijing ta zama wata taga da kasashen duniya suke fahimtar kasar Sin, a sa'i daya kuma, ta samar wa kasashen duniya wata kyakkyawar damar kara fahimtar juna, da zurfafa amincin dake tsakaninsu.
Shugaban majalisar jama'a ta kasar Masar Ahmed Sathy Sorour ya bayyana cewa, kasashen duniya sun yi mamaki da ganin nasarar da kasar Sin ta samu a wasani da aikin shiryawa. Wannan ya shaida cewa, kasar Sin tana iya shirya babbar gasar wasan motsa jiki, ban da wannan kuma, babban ci gaba da kasar Sin mai dogon tarihi ta samu.
Shugaban kwamitin kasar Amman Mr. Yahya Bin Mahfoodh Al-Manthri ya bayyana cewa, kasar Sin ta mai da hankali sosai wajen aikin shirya wasannin gasar wasannin Olympic nan, musamman wasani masu ban sha'awa da aka gabata a bukukuwan budewa da refuwa, ya nuna yabo sosai a kai.
Shugaban majalisar dokoki na kasar Indonesia Mr. Agung Laksono yana fatan gasar wasannin Olympic ta Beijing ta samar da wata muhimmiyar damar tattaunawa, da kara fahimta, da inganta zaman lafiya da jituwa ga kasashen duniya.
Shugaban kasar Brazil Mr. Luiz Inacio Lula Da Silva ya bayyana cewa, babu aibi ko kadan a cikin aikin shirya gasar wasanninOlympic ta Beijing. Shugaban kasar Botswana Mr. Seretse Khama Ian Khama ya yaba da gasar wasannin Olympic ta Beijing sabo da ta kara fahimtar juna tsakanin jama'ar kasa da kasa ta hanyar wasanin motsa jiki da duk mutanen duniya ke iya shiga a ciki. Babban sakataren kungiyar ASEAN Mr. Surin Pitsuwan ya ce, gasar wasannin Olympic ta Beijing ta zama sabuwar alama a cikin tarihin wasannin Olympic.
Ban da wannan kuma, ministan harkokin waje na kasar Argentina Mr. Jorge Taiana da takwaransa na kasar Kenya Mr. Moses Wetangula sun ma su aiko sakonin taya murna ga kasar Sin. (Zubairu)
|