Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-10 16:40:32    
Bisa taimako daga CRI, 'yan wasa na kasar Uganda sun samu tufafi masu bai daya

cri

A 'yan kwanakin baya, 'yan wasa na tawagar wakilai ta wasanni ta nakasassu ta kasar Uganda sun karbi tufafin wasanni masu bai daya da wani kamfanin wasanni na kasar Sin ya bayar gare su a kauyukan Olympics na nakasassu na Beijing. Bayan da ya sanya irin wadannan tufafi, 'dan wasan daukar nauyi na kasar Uganda Mr. Ssengendo Billy ya nuna godiya ga taimakon da abokansa na kasar Sin suka ba su, ya ce, da ya sanya tufafi masu bai daya, ya kara jin karfi a jikinsa.

A gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing, 'yan wasa na tawagar wakilai ta wasanni ta nakasassu ta kasar Uganda ba su da tufafi masu bai daya, 'yan wasa suna sanya tufafi na zaman yau da kullum a yayin da suke halartar bikin bude gasar wasannin Olympics da kuma shiga cikin gasanni, bisa taimako daga gidan rediyon kasar Sin wato CRI da gidan rediyo mai hoto wato CCTV, wani kamfanin wasanni na kasar Sin ya bayar da tufafin wasanni masu bai daya a matsayin kyaututtuka ga tawagar kasar Uganda.(Danladi)