Yau ran 9 ga wata, an shiga rana ta 3 da soma gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing, za a fitar da lambobin zinariya guda 61 a cikin gasannin tsalle-tsalle da guje-guje da iyo, za ta zama ranar dake fitar da lambobin zinariya mafi yawa a gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing.
Da ya zuwa ran 8 ga wata, kasar Sin ta samu lambobin zinariya guda 8, shi ya sa, ta zama kasar dake da lambobin zinariya mafi yawa.
A cikin gasani da aka shirya a yau, za a fitar da lambobin zinariya guda 4 a cikin gasannin boccia. Uku daga yan wasa na kasar Sin 9 sun kai matsayi na daya zuwa na 8.
Ran nan, wasan Judo na makafi zai shiga zagayen karshe, za a fitar da lambobin zinariya guda 5. Za a fara gasar wasan daukan nauyi ta nakasussu a hukunce. Ban da wannan kuma, za a fitar da lambobin zinariya guda 16 a cikin gasannin iyo.
Kazalika kuma, za a fitar da lambobin zinariya guda 20 a cikin gasannin tsalle-tsalle da guje-guje. Kuma za a ci gaba da yin gasannin wasan Gateball na nakasassu, da kwallon kwando, da wasan takobi na nakasassu. (Zubairu)
|