Mataimakin firayin ministan kasar Sin Mr. Li Keqiang ya bayyana a ran 8 ga wata a birnin Beijing cewa, kasar Sin za ta yi kokarin da take iya yi domin shirya gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing da kyau, domin samar da wani dandamali ga 'yan wasa na nakasassu da su wuce karfin da bil-adam suke da shi, da kuma nuna darajarsu, bugu da kari kuma za a sa kaimi ga bunkasuwar sha'anonin nakasassu na kasar Sin bisa wani sabon masomi.
Mr. Li ya yi wannan bayani ne a yayin da yake zantawa da mataimakiyar firayin ministan kasar Croatia Madam Jadranka Kosor, wadda take birnin Beijing domin halartar bikin bude gasar wasannin Olympcis ta nakasassu ta Beijing da sauran aikace aikace. A ganin Madam Kosor, kasar Sin za ta samu nasarar shirya gasar wasannin Olympcis ta nakasassu ta Beijing kamar yadda ta gudanar da gasar wasannin Olympics ta Beijing.(Danladi)
|