A yayin da shugaban hukumar wasannin Olympics ta nakasassu ta duniya Mr. Philip Craven yake zantawa da manema labaru na gidan rediyon kasar Sin a ran 8 ga wata, ya bayyana cewa, gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing ta shekarar 2008 za ta samar da kyawawan kayayyakin tarihi ga kasar Sin.
A ganin Mr. Craven, samun nasarar shirya gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing ta shekarar 2008, zai samar da kyawawan kayayyakin tarihi ga birnin Beijing da duk kasar Sin, wadanda kuma za su bayar da moriya ga nakasassu da yawansu ya kai miliyan 83 na kasar Sin cikin dogon lokaci. Da farko dai, gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta bayar da filaye da dakunan wasanni na musamman da kuma cibiyoyin warkar da nakasassu. Na biyu, gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta Beijing za ta sa kaimi ga kafa na'urori marasa shinge a birnin Beijing da dukkan biranen kasar Sin, ta yadda nakasassu za su iya samun saukin tafiya zuwa waje.(Danladi)
|