Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-08 16:06:03    
Hu Jintao da Wu Bangguo da Wen Jiabao sun aika da sakon taya murnar cika shekaru 60 da kafuwar kasar Koriya ta arewa

cri
Ran 9 ga wata rana ce ta cika shekaru 60 da kafa jamhuriyyar jamar dimokuradiyyar kasar Koriya ta arewa. Ran 8 ga wata, a madadin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da gwamnatin Sin da jama'arta, Hu Jintao, shugaban kasar Sin, da Wu Bangguo, shugaban zaunannen kwamiti na majalisar wakilan jama'ar Sin, da Wen Jiabao, firayin ministan majalisar gudanarwa ta kasar Sin sun aika da sako ga Kim Jong-il, babban sakataren jam'iyyar aiki ta Koriya ta arewa kuma shugaban kwamitin tsaron kasar da Kim Yong-nam, shugaban zaunannen kwamitin majalisar jama'a ta koli na Koriya ta arewa da Kim Yong-il, firayin ministan majalisar ministoci domin taya wa jam'iyyar aiki ta kasar da gwamnatin kasar da jama'arta murna da nuna fatan alheri.

A cikin sakon, an bayyana cewa, a cikin shekaru 60 da suka gabata, a karkashin shugabancin shugaba Kim il sung da babban sakatare Kim Jong-il da jam'iyyar aiki ta Koriya ta arewa, jama'ar Koriya ta arewa sun yi aiki da dogara da karfinsu na kansu da kuma yi aiki wurjanjan, har sun samu nasarori masu dimbin yawa a cikin juyin hali da raya kasa na mulkin gurguzu. Kasar Sin ta yi farin ciki da ganin haka, kuma tana fatan jama'ar Koriya ta arewa za su samu sabuwar nasara a fannin bunkasa tattalin arziki da zamantakewar alumma da inganta mu'amala da hadin gwiwa tare da kasashen waje da sauransu.

Sakon taya murna ya ce, bangaren Sin yana fatan yin kokarin ba tare da kasala ba tare da bangaren Koriya ta arewa wajen ciyar da dangantakar hadin gwiwa ta sada zumunta tsakaninsu gaba da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a bangaren nan.

Sakon ya yi fatan jamhuriyyar jama'ar dimokuradiyyar kasar Koriya ta arewa ta samu wadatuwa da jama'arta na zaman jin dadi.(Fatima)