Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-08 14:55:48    
An bude makarantun firamare da na midil a Panzhihua a ran 8 ga wata

cri
Ran 8 ga wata, a yankin Panzhihua na lardin Sichuan na kasar Sin, 'yan makarantun firamare da na midil dubu 200 sun koma makaranta bayan an jinkirta komawar tasu makaranta sabo da girgizar kasa.

An samu girgizar kasa mai karfin digiri 6.1 bisa ma'aunin Richter a yankin Panzhihua da huili a lardin Sinchuan da ke kudu maso yammacin kasar Sin a ran 30 ga watan Agusta.Bisa wannan dalili ne, gwamnatin birnin Panzhihua ta ba da sanarwar jinkirta lokacin sake bude makarantun firamare da na midil daga ran 1 ga wata zuwa ran 8 ga wata.

Bisa labarin da manema labaru suka sami, an ce, gine-ginen makarantu 183 sun lalace sabo da girgizar kasar a Panzhihua, ana bukata tsugunar da kashi daya cikin kashi biyar na 'yan makaranta a wuraren daban ko a tantuna domin su cigaba da karatunsu.

Kong Wei, shugaban hukumar ilmi ta birnin Panzhihua ya bayyana cewa, sun dauki muhimman matakai 3 domin tabbatar da bude makarantu a ran 8 ga wata, wato na farko shi ne a kara yawan 'yan ajin karatu, na biyu shi ne tsugunar da wasu a wurare daban, na uku shi ne kafa tantuna da dakunan wucin gadi.

Kong Wei ya bayyana cewa,sun sami taimako da dama bayan da makarantun ilmi suka yi kira ga alumma da su ba da tantuna ga makatantun firamare da na midil da bala'in girgizar kasa ya lalata ta kafofin watsa labaru, a cikin gajeren lokaci an daidaita matsalar tantuna.(Fatima)