Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-09-07 20:27:34    
Firaministan kasar Sin ya gana da takwaransa na Koriya ta kudu

cri
Yau 7 ga wata a nan birnin Beijing, firaministan kasar Sin, Wen Jiabao ya gana da takwaransa na Koriya ta kudu, Mr.Han Seung-soo, wanda ya zo kasar Sin, domin halartar bikin fara wasannin Olympic na nakasassu na shekarar 2008.

Mr.Wen Jiabao ya ce, Sin na fatan wasannin Olympics na nakasassu za su iya karfafa gwiwar nakasassu da su kara sa hannu cikin harkokin zaman al'umma, kuma a kyautata tunanin al'umma dangane da ba da taimako ga saura, ta yadda za a kara samun kaunar juna da walwala a duniya.

Daga nasa wajen kuma, Mr.Han Seung-soo ya ce, gwamnatin kasar Sin da jama'arta sun yi namijin kokari wajen gudanar da wasannin Olympic da wasannin Olympic na nakasassu kamar yadda ya kamata a birnin Beijing, kuma sun sami girmamawa sosai daga wajen al'ummomin duniya. Mr.Han Seung-soo ya kuma darajanta muhimmiyar rawar da Sin ke takawa a wajen shawarwarin bangarori shida kan batun nukiliyar zirin Koriya.(Lubabatu)