|
|
|
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
|
|
|
|
|
|
(GMT+08:00)
2008-09-07 19:17:37
|
Shugabanni daga kasashen Jamus, Swiss sun kai ziyara a kauyen wasannin Olympics na nakasassu
cri
A ranar 7 ga wata, daya bayan daya shugaban kasar Jamus Horst Koehler, da ministan tsaron kasa, kuma ministan motsa jiki na kasar Swiss Samuel Schmid sun kai ziyara a kauyen wasannin Olympics na nakasassu.
Mataimakiyar shugaban kwamitin shirya wasannin Olympics na Beijing, kuma shugabar kauyen wasannin Olympics na nakasassu na Beijing madam Chen Zhli ta nuna maraba sosai ga zuwan baki. Bayan haka kuma, ta yi godiyar musamman ga gwamnatin kasar Jamus da ta bayar da taimako kan bala'in girgizar kasa da ta auku a lardin Sichuan, da ayyukan share fage na wasannin Olympics na nakasassu na Beijing. Ta bayyana cewa, kasar Sin za ta yi amfani da dama mai kyau ta shirya wasannin Olympics na nakasassu na shekarar 2008, don kara jawo hankulan duk kasar kan nakasassu, har ma da ciyar da sha'annin nakasassu gaba. (Bilkisu)
|
|
|